Peace Corps ta Nigeria (PCN), sun maka babban mai shari’a na kasa, Babban sufeton ‘yan sanda na kasa, da kuma darakta janar na Jami’an tsaron sirri na DSS a bisa kamun Kwamandan Peace Corps na kasa (Dr.) Dickson Akoh da kuma wasu mutane 49 sakamakon rufe Hedikwatar su ta kasa da kuma rufe ofisoshin su da ke sauran jihohi ba bisa ka’ida ba.
Sannan sun nemi da a basu diyyar kudi har naira biliyan 2 bisa cin zarafin da akai musu ba bisa ka’ida ba