
Asalin hoton, Alamy
Pelé ya ziyarci kasar Kenya a shekarun 1970
Kasancewarsa daya daga cikin manyan taurarin matasan bakaken fata a fagen wasanni a zamanin talabijin, Pelé ya samu karbuwa da kauna daga ‘yan Afirka a fadin nahiyar.
A lokacin da kasashen Afirka ke fafutukar samun ‘yancin- kai a karshe-karshen shekarun 1950 da kuma farko-farkon 1960, Pelé ya rika samun gayyata daga kasashen Afirka da suka samu ‘yanci, domin wasan sada zumunta da kungiyarsa Santos FC da kuma tawagar kasarsa ta Brazil.
A tarihinsa da ya rubuta, Pelé ya bayyana cewa wadannan tafiye-tafiye da ya rinka yi zuwa kasashen Afirka a wannan lokaci ba kawai sun sauya yadda yake kallon duniya ba har ma da yadda ya ce duniya ta dauke shi.
Mutumin da ya rubuta kundin kungiyar kwallon kafa ta Santos, Guilherme Nascimento, ya yi daidai kamar yadda ya nuna cewa wadannan tafiye-tafiye zuwa Afirka na cike da labarai wadanda kusan da wuya a iya bambancewa tsakanin na gaskiya da kuma na kunne-ya-girmi-kaka.
Zuwan Pelé Algeria, a misali ya kasance kamar wani abu na fim. A shekarar 1965, tauraron wanda a lokacin yana da shekara 24 ya je kasar a daidai lokacin da darektan fim, Gillo Pontecorvo yake hada fim din ”The Battle of Algiers”.
A don haka sai abin ya zo daidai da lokacin da za ka ga tankokin yaki suna ta kai-komo a fadin kasar kama daga kauyuka zuwa Casbah.
Shugaban kasar na wannan lokaci Ahmed Ben Bella, mai matukar sha’awar wasan kwallon kafa ya shirya wasan sada zumunta biyu domin wannan ziyara.
Daya a Oran a ranar 15 ga watan Yuni, dayan kuma a babban birnin kasar, Algiers, bayan kwana hudu.
Sai dai kuma ministan tsaro na lokacin Houari Boumediene ya yi juiyin mulki inda ya hambarar da Shugaba Ben Bella, saboda haka ya soke daya wasan sada zumuntar.
Wasu ‘yan jarida da fashin baki sun ce ministan ya yi amfani da yanayin da ake ciki na ruguguguwa da murnar zuwan tauraron kwalon kafar, a matsayin wata hanya ta dauke hankali ya yi juyin mulkin.
Asalin hoton, Getty Images
Pele da tsohon tauraro kuma yanzu shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru Samuel Eto’o na gaishe da ‘yan kallo a wasan martaba Nelson Mandela a 2007
Sai dai tarin ziyarar da Pele ya rika kaiwa Moroko a matsayinsa na tauraron kwallon kafa a lokacin ba su kai kamar na wasu ba.
An ce ya yi wasu kalamai masu dadadawa da yabo ga tawagar kasar da ta je gasar cin Kofin Duniya a 1970 a Mexico, kasancewar ita ce kasa ta farko a Afirka da ta fara samun gurbin wannan gasa ta duniya tun bayan Masar a 1934.
A lokacin wata ziyarar kuma an ce Pele ya yi magana a kan tauraron kwallon kafar kasar ta Moroko na zamanin wato Larbi Ben Barek, wanya ya taka leda a Olympique de Marseille da Atletico Madrid.
Ya ce, “Idan ni ne sarkin kwallon kafa to kuwa Ben Barek shi ne uban-gijinta.” Kamar yadda aka ce ya ce.
Sai an bayar da murfin kwalba shida a kalli Pele
Ziyarar Pele zuwa Najeriya da kuma Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo ita ma ta kasance cike da labarai iri-iri ko dai na gaskiya ko kuma na kanzon-kurege.
A lokacin zuwansa kasashen biyu an ce ya sa an samu dakatar da bude wuta a kasashen masu karbar bakuncinsa yakin basasa da suke yi.
An yi yakin basasar Najeriya daga shekarar 1967 zuwa 1970, amma duk da haka ana cewa lokacin da ya je domin wani wasa na karramawa da tawagar kwllon Najeriya, an dakatar da bude wuta a yakin tsawon sa’a 48.
Sai dai Pelen da kansa a littafinsa ya rubuta cewa, ” Ba ni da tabbacin cewa lalle gaskiya ne.”
Amma ya kara da cewa, “Amma fa ‘yan Najeriyar lalle sun dauki matakan tabbatar da cewa ‘yan Biyafara ba su mamayi Lagos ba a lokacin da muke can,” yana mai tuna irin tarin sojojin da aka baza a birnin.
Ana wannan magana ce kuwa duk da cewa fa ba ta yadda ‘yan awaren na Biyafara za su iya yin hakan domin suna nisan akalla kilomita 500 ne tsakaninsu da Lagos, hasali ma sojojin Najeriya suna tura su baya a lokacin.
A shekarar 1976, kamfanin lemon kwalba na Amurka, Pepsi ya yi amfani da farin jinin Pele a nahiyar Afirka wajen tallata lemon, inda ya dauki nauyin ziyarar tauraron zuwa Afirka ta Gabas, a kasashen Kenya da Uganda.
A lokacin Sarkin Kwallon kamar yadda ake masa lakabi ya yi nasarar tallata lemon tare da gudanar da wasu sansanoni na matasan ‘yan wasa a kasashen biyu.
A Kenya sai ‘yan kallo sun bayar da murfin kwalbar lemon kafin su shiga kallo, inda manya suke bayar da shida yara kuma uku.
Asalin hoton, Getty Images
Pele da Shugaban Gabon Ali Bongo lokacin kaddamar da mutum-mutuminsa a 2012
A duk tsawon wadannan shekaru, Pelé ya kuma ziyarci kasashen Mozambique da Masar da Sudan da Senegal da kuma Ghana.
Bayan ziyarce-ziyarcen masu tarihi, Pelé ya kasance wata alama ta karfafaguiwa da zama abin koyi ga ‘yan kwallon kafa masu tasowa a nahiyar Afirka.
“A lokacin da na je Turai, mu ‘yan Afirka Pele da Mohamed Ali da kuma Eusébio kawai muke da a matsayin wasu fitattun taurari,” a cewar tsohon dan kwallon kafar Mali, Salif Keita.
Har ma daya daga cikin fitattu kuma manyan gwarazan ‘yan kwallon kafa na Ghana, ya lakaba suna Pele a cikin sunansa inda ake kiransa da Abedi “Pele” Ayew.
Gwarzon na Ghana, ya ce, ” Daukakarsa ta karfafa min guiwa, wanda hakan ya sa na dauki sunasansa na yi lakabi da shi domin na zama kamarsa a tsawon rayuwata ta kwallon kafa, har ma bayanta, wnda wannan ba karamar daraja ba ce,” kamar yadda ya gaya wa BBC.
Har kullum Pelé ya kasance mai kyakkyawan fata da kishin ci-gaban Afirka a gasar Kofin Duniya.
Hasashen da ya yi a tsakiyar shekarun 1970 cewa wata kasar Afirka za ta ci Kofin Duniya kafin shekara ta 2000, ya kasance abin tattaunawa sosai kafin fara duk wata gasa ta Kofin Duniya tun daga lokacin da ya yi furucin.
A don haka abu ne da ya yi daidai kasancewar sakonninsa na karshe a shafukan intnet sun hada da na taya murna da ya yi ga kasar Moroko kan rawar da ta taka ta a-zo-a-gani wadda ta kasance tarihi a gasar Kofin Duniy da aka yi a Qatar.
“Ba zan kasa taya Moroko murna ba a kan gagarumin kokarin da suka yi.
Abin alfahari ne a ga Afirka ta yi fice.” Kamar yadda ya rubuta a sakon.