Pele: Mashahurin ɗan wasan da ya fito da hasken ƙwallon ƙafa a duniyaPele

Asalin hoton, Getty Images

Bobby Charlton, wani tsohon fitaccen ɗan ƙwallon Ingila ya taɓa cewa mai yiwuwa “saboda shi (Pele) aka ƙirƙiri ƙwallon ƙafa”.

Tabbas, mafi yawan masu sharhi suna ɗaukan sa a matsayin gangariyan mai rajin buga ƙwallon ƙafa mafi ƙayatarwa.

Ƙwarewar Pele da saurinsa kamar walƙiya sun haɗu da mayataccen saitin da yake da shi idan ya tsaya a kan ƙwallo.

Wani gwarzon ƙasa ne a mahaifarsa Brazil, kuma ya zamto mashahurin ɗan wasan duniya.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like