Pfizer za ta tallafa wa Afirka da maganin corona | Labarai | DWKasashen nahiyar Afirka za su samu wadatattun magungunan cutar corona nan bada jimawa ba, hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da manyan kamfanonin harhada magunguna a nahiyar suka cimma da katafaren kamfanin harhada magunguna nan na Pfizer.

Shugaban wata cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika, John Nkengasong ne ya tabbatar da labarin cimma yarjejeniyar a wannan Alhamis. Jami’in ya ce, da zarar sun kamalla shirin da kamfanin na Pfizer, za su yi wa jama’a karin bayani.

A dai fafutukar da aka jima ana yi na yakar annobar corona da ta bulla a Disambar shekarar 2019 da ta kuma lakume rayuka kusan miliyan shida, nahiyar Afirka ta kasance a sahun baya a fannin samun magunguna dama allurar riga-kafin cutar.
 You may also like