Pogba ya kara jin rauni a karon farko da Juve ta fara wasa da shiJuventus

Asalin hoton, Getty Images

Paul Pogba ya ji rauni a karawar farko da Juventus ta fara wasa da shi a kakar nan, wadda ta doke Cremonese ranar Lahadi.

Pogba mai shekara 30 ya ji raunin a minti na 24 da fara wasa a gasar ta Serie A, inda dan kwallon Faransa ya rufe fuska yana kuka a wasan da Juve ta ci 2-0.

Shine karon farko da Pogba aka fara wasa da shi tun bayan fafatawar da ya buga wa Manchester United da Liverpool a Afirilun 2022.

A fafatawar ce ya ji raunin da ya yi jinya zuwa karshen kakar tamaula.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like