
Asalin hoton, Getty Images
An kara samun jinkiri kan lokacin da ya kamata Paul Pogba ya fara buga wa Juventus tamaula a bana, in ji koci Massimiliano Allegri.
“Pogba ba zai buga mana wasa ranar Lahadi ba da Fiorentina,” kamar yadda Allegri ya sanar da manema labarai ranar Asabar.
”Yana ta kokari ya koma buga mana wasanni, ba zan iya tabbatar da ranar da zai koma taka leda ba.”
Dan kwallon tawagar Faransa bai yi wa Juventus wasa ba tun bayan da ya koma Italiya kan fara kakar bana daga Manchester United.
Dan wasan ya ji rauni ne a cikin watan Yuli a gwiwar kafarsa ta hadu.
Tsohon dan wasan United bai yi wa Faransa gasar kofin duniya da aka yi a Qatar ba, wanda Argentina ta lashe, bayan cin Faransa a bugun fenariti.
A karshen watan Janairu lokacin da Juventus ke shirin karawa da Monza, Alegri ya sanar cewar Pogba ya fara atisaye, amma bai kai ya buga wasa ba.
A ranar ta Asabar, Allegri ya ce zai kara sanin lokacin da ya kamata dan wasan zai koma murza leda nan gaba, watakila nan da mako uku.
Juventus wadda aka kwashe mata maki 15, tana ta 11 a teburin Serie A da tazarar maki 30 tsakaninta da Napoli, wadda take ta daya.
Ranar Talata, Juventus za ta karbi bakuncin Nates a wasan farko a neman gurbin shiga Europa League zagayen ‘yan 16.