
Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Portugal ta gayyaci Cristiano Ronaldo, domin ya buga mata wasannin neman shiga gasar Euro 2024.
A cikin watan Maris, Porugal za ta fafata da Liechtenstein da kuma Luxembourg a wasannin neman shiga gasar nahiyar Turai.
Da an dora alamomin tambaya kan makomar dan wasan mai shekara 38 a Portugal, bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.
Dan kwallon ya bar cikin filin wasa yana kuka, bayan da Morocco ta fitar da Portugal a karawar daf da na kusa da na karshe a gasar.
Tuni Portugal ta dauki Roberto Martinez, wanda ya maye gurbin Fernando Santos, bayan kofin duniya, shi kuwa Martinez ya mika goron gayyata ga Ronaldo.
Martinez ya fada cewar ”Ronaldo dan wasa ne mai mahimmaci a tawagar” bana kallon yawan shekarunsa.”
Portugal za ta karbi bakuncin Liechtenstein ranar 23 ga watan Maris, sannan kwana uku tsakani ta ziyarci Luxembourg.
Ronaldo ya ci kwallo 118 a karawa 196 da ya yi wa Portugal.
Tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus ya bar Manchester United a cikin watan Nuwamba zuwa Al Nassr ta Saudi Arabia a watan Janairu.
Kawo yanzu ya ci kwallo takwas a wasa tara a Al Nassr.