Portugal za ta kara da Wales a wasan daf da karshe


Portugal vs Wales Live Stream Highlights

 

A ranar Laraba tawagar kwallon kafa ta Porugal za ta kece raini da ta Wales a wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai da ake yi a Faransa.

Portugal ta kai wannan matakin ne bayan da ta ci Poland 5-3 a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a wasan daf da na kusa da karshe a ranar Alhamis.

Ita kuwa Wales ta kai wasan zagayen gaba ne,bayan da ta doke Belgium da ci 3-1 a ranar Juma’a.

Kasashen sun kara sau uku a tsakaninsu, amma ba su taba haduwa ba a babbar gasa, inda Portugal ta ci karawa biyu a baya, Wales kuwa ta ci wasa daya a shekarar 1951.

Rabon da kasashen su kara tun wasan sada zumunta da suka yi a shekarar 2000, kuma Portugal ce ta ci wasan da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a Chaves.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like