
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaban Tottenham daga Ingila Harry Kane mai shekara 29, shi ne babban burin ƙungiyar Paris St-Germain na samun ɗan gaba mai cin ƙwallo a lokacin kaka. (Le Parisien)
Hukumar gudanarwar Liverpool ta shirya kuma ta amince da wani kwanturagi ga ɗan wasan tsakiya na Ingila da ke buga wa Chelsea, ƙwallo wato Mason Mount ɗan shekara 24. (Football Insider)
Koci Jose Mourinho na iya zama manajan Paris St-Germain a kakar wasanni mai zuwa saboda mai horas da kulob ɗin na Roma a yanzu shi ne a sahun gaba cikin jerin mutanen da daraktan wasanni na PSG Luis Campos ke fatan ɗauka. (RMC Sport)
Akwai ƙarin yiwuwar koci David Moyes zai iya barin West Ham a lokacin bazara, yayin da shugabannin ƙungiyar suka fara ƙoƙarin tantance manajan da suke fatan zai maye gurbinsa. (Mail)
Crystal Palace na son Roy Hodgson ya ci gaba da zama a kulob ɗin har zuwa kakar wasanni ta gaba don ya riƙa bai wa duk mutumin da zai maye gurbinsa shawarwari. (Telegraph)
An ba da rahoton cewa Steven Gerrard yana cikin jerin koci-koci da kulob ɗin Olympiakos na ƙasar Girka ke son ɗauka, wata shida bayan ƙungiyar Aston Villa ta sallame shi. (Express)
Manchester United da Liverpool na kan gaba a rige-rigen ɗaukar ɗa wasan tsakiya na Brighton daga Argentina Alexis Mac Allister, an kasa samun wani ci gaba a tattaunawa kan matashin ɗan shekara 25 da Arsenal. (Cesar Luis Merlo – on Twitter)
United na kusantar cimma yarjejeniya kan wani sabon kwanturagi da golanta na ƙasar Sifaniya David de Gea, ɗan shekara 32, wanda kwangilarsa ta yanzu za ta ƙare a ƙarshen kakar nan. (ESPN)
Southampton ta shaida wa ɗan wasanta na tsakiya James Ward-Prowse, mai shekara 28, cewa yana iya tafiya da bazara idan kulob ɗin ya faɗa ƙasa daga Gasar Firimiya a ƙarshen kaka. Tottenham da West Ham da kuma Newcastle duk suna nuna sha’awa kan ɗan ƙwallon duniyar na ƙasar Ingila. (Talksport)
Leeds za ta rattaba hannu kan yarjejeniya don ɗaukar ɗan wasan gefe na Sifaniya da ke buga wasa a matakin ‘yan ƙasa da shekara 19 Ilias Akhomach, bayan matashin ɗan shekara 19, ya gaza daidaitawa da Barcelona wadda ta buƙaci ya sabunta kwanturagi. (Sport )
Kulob ɗin Barcelona yana daɗa ƙarfafa imani cewa ɗan ƙwallon gaba na ƙasar Argentina mai buga wa Paris St-Germain Lionel Messi, da ke da shekara 35, zai sake koma wa ƙungiyar a cikin bazara. (Sport – in Spanish)