PSG ta yi wa Real Madrid kancal a kan Mbappe, AC Milan za ta saki IbrahimovicKylian Mbappe

Asalin hoton, EPA

Paris St-Germain ta yi wa Real Madrid kancal a burinta na daukar Kylian Mbappe a bazara, inda ta gaya mata cewa ba za ta sayar da dan gaban na Faransa ba kafin 2024. (Sport)

Haka kuma PSG din za ta sake yunkurin neman dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech, na Morocco a bazara. (Football Insider)

Chelsea za ta duba yuwuwar zawarcin Carlo Ancelotti a karo na biyu idan kociyan ya kammala aikinsa da Real Madrid a karshen kaka. (ESPN)

Wakilin Sofyan Amrabat ya ce Fiorentina za ta saurari tayi daga masu sha’awar sayensa a bazara kuma tuni Manchester United ta gabatar da bukatarta ta sayen dan Moroccon a watan Janairu. (Sport)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like