Putin ya ci zabe da zai sake bashi damar wa’adin mulki na tsawon shekaru 6


Shugaban kasa Vladmir Putin na kasar Russia ya sake cin zabe da zai ba shi damar kasancewa akan mulki na tsawon shekaru 6.

Putin wanda ya  lashe zaben bayan da ya samu kaso 75 na kuri’ar da aka kada.

Babban jagoran yan adawa, Alexei Navalny an hana shi tsayawa takara a zaben ya yin da Pavel Grudinin na jami’iyar kwaminisanci ya samu kaso 11.2 na kuri’un da aka kada.

Ana nuna  shakku kadan kan sakamakon duba da yadda fadar mulki ta Kremlin take rike gam da bangarorin dake taimakawa wajen tafiyar da mulki ciki har da gidajen talabijin da yan  kasar suka fi kallo.

A lokaci guda Putin wanda farin jininsa ya kai kaso 80 cikin dari ya fuskanci adawa daga yan takarar da yawancinsu ba sanannu bane da kuma wasu yan takarkaru da basu taba tsayawa takarar zaɓe ba.

Saboda haka, tambayar dake bakin mutane kafin zaben ita ce yawan mutane da za su fito kada kuri’a ya yin da fadar Kremlin ta so cewar mutanen su haura kaso 65 cikin dari na yadda suka fito  a zaben shekarar 2012.

Da yakewa wani taron gangami jawabi a birnin Moscow bayan da sakamakon farko ya fara bayyana Putin ya ce masu kada kuri’a sun gane “cigaban da aka samu a cikin shekarun da suka wuce.”

You may also like