
Asalin hoton, AFP
Wani yaro dan shekara 14 ya rasa ransa bayan da mota tabi ta kansa a birnin Montpellier da ke kudancin Faransa.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala wasan kusa da karshe da Faransa ta yi nasara kan Maroko.
Hukumomi sun ce wata mota ce manne da tutocin Faransa a jikinta, tazo a guje ta bi ta kan yaron, kuma ya mutu ne a asibiti.
Yanzu haka yan sanda na kan neman direban motar.
Dama jim kadan bayan kammala wasan an samu hatsaniya tsakanin magoya bayan Faransa da takwarorinsu na Maroko a wasu anguwannin tsiraru.
Sai dai yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wurin tarwatsa su.
Akwai kusan mutum miliyan daya da rabi yan Maroko mazauna Faransa.
Ko a birnin Lyon an samu barkewar tarzoma, kuma an girke yan sanda 10,000 tare da kama mutum 167 a fadin kasar.