
Asalin hoton, AFP
Croatia ta kammala zamanta a Qatar bayan da ta lashe matsayin na uku a nasarar da ta yi kan Maroko.
An tashi wasan 2-1, kuma an ci kwallayen ne tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Croatia ce ta fara cin kwallo ta hannun dan bayanta Gvardiol, amma tun ba a je ko’ina ba Dari ya farkewa Maroko.
Ana kuma dab da zuwa hutun rabin lokaci ne Orsic ya ci wa Croatia kwallo ta biyu.
Sai dai bayan an dawo hutun rabin lokaci Maroko ta yi ta kokarin ganin ta farke amma hakan bata yiwuwa ba.
An rika samun rashin jituwa tsakanin yan wasan na Atlas Lions da mai busa wasa bayan da suka yi zargin yana nuna musu bambanci.
To amma a karshe wasan ya tashi 2-1 duk da matsin da Marokon ta rika kaiwa.
Croatia ce ta buga wasan karshe a gasar kofin duniya ta 2018, kuma a Qatar 2022 ta kammala tafiyarta a na uku.
A gobe Lahadi ne za a buga wasan karshe tsakanin Argentina da Faransa a filin wasa na Lusail da karfe hudu agogon Najeriya.