
Asalin hoton, EPA
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya ce babu rayuwar da aka rasa ta yan ci rani da suka yi aikin gina filayen wasa a Qatar, da duniya ba ta yi bakin ciki ba.
Da yake martani game da tambayar da aka masa kan batun, Infantino ya ce mutuwar tasu a bakin aiki rashi ne ga iyalansu da kuma kowa da kowa.
Sai dai ya ce wasu kafafen yada labarai na zuzuta batun don bata sunan wasu.
”Mutum 400 zuwa 500 ne suka mutu yayin aikin gina filaye daga 2014 zuwa yanzu. Idan muna magana kan alkaluma, yakamata mu rika tabbatar da cewa mun fadi ainihin gaskiyar.”
”Yakamata mu yi hattara kar mu fadi abunda ba shi ba da zai iya haifar da wani abu daban ga idon al’umma”, in ji Shugaban na FIFA.
Wasu kasashen Yamma sun sha sukar Qatar kan mace macen yan ci rani da suka mata aikin gina filayen da ake buga wasan kofin na duniya.
To amma shugaban FIFA yayin hira da menama labarai dab da fara gasar, ya bayyana cewa kasashen turawa munafukai ne.