
Asalin hoton, OTHER
Kwamitin da ke jagorancin alkalan hukumar kwallon kafa ta duniya, ya zabi Szymon Marciniak a matsayin lafarin da zai busa wasan karshe tsakanin Faransa da Argentina.
Dan kasar Poland din mai shekaru 41, na cikin tawagar alkalan da suka jagorancin wasannin kasashen biyu kafin a kawo wannan mataki na wasan karshe.
Akwai wasan da Argentina ta doke Australia a zagayen kwaf daya, da kuma wanda Faransa ta doke Denmark a wasan rukuni.
Jiya Alhamis ne FIFA ta sanar da sunansa a matsayin wanda zai raba gardama, a wasan da duniya ke dakon gani tuntuni.
Ana yi wa Szymon Marciniak kallon lafari mafi shahara a Poland da ma daukacin Turai, kuma kwarewarsa tasa hukumar kwallon kafar Turai ta bashi bushin wasan karshe na Uefa Super Cup.
Kazalika FIFA ta bayyana sunayen Pawel Sokolnicki da Tomasz Listkiewicz, wadanda dukansu suma yan Poland ne, a matsayin masu taimaka masa.
Ga al’ada a kan bai wa tawagar masu bushi zinariya kafin bada kofi ga kasar da ta yi nasara.
Ranar Lahadi ne za a buga wasan na karshe a filin Lusail da ke Doha tsakanin kasashen biyu, to amma kafin nan sai an buga neman na uku tsakanin Maroko da Croatia.