
Asalin hoton, OTHER
Yan wasan Faransa da dama sun kamu da sanyi a sansaninsu da ke Doha gabanin wasan karshe da za su buga da Argentina ranar Lahadi.
Na baya bayannan sune masu tsaron baya Raphael Varane da Ibrahim Kounate, wadanda rashin lafiyar ta hana su yin atisaye.
Dama mai tsaron baya Dayot Upamecano da dan wasan tsakiya Adrien Rabiot ba su samu buga wasan kusa da karshe ba da Faransa ta yi nasara kan Maroko.
Dan wasan gaba Randal Kolo Muani ya ce wadanda suka kamun suna nan killace dakunansu.
Faransa za ta kara da Argentina ne a wasan karshe na kofin duniya da karfe 4:00 agogon Najeriya, karfe 3:00 agogon GMT.
”Wadanda basu da lafiya na dakunansu.” in ji Kolo Muani. ”Likitoci na ci gaba da kula dasu kuma ana tabbatar cewa ana ba da tazara.”
A ranar Laraba koci Didier Deschamps ya ce yana sa ran Upamecano da Rabiot za su warke su buga wasan karshe.
To amma kuma idan har Konate da Varane suka kasa, zai samu matsalar wa zai saka, saboda irin tasirin da suke da shi a tawagar.