Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Najeriya Kan Ganawar Shugaba Tinubu Da Biden
LEGOS, NIGERIA – Wasu batuwa da akesa ran za’a tattauna a wajen taron dai sun hada da batun dumamar yanayi da yakin Ukraine da Rasha da sauran matsaloli na tattalin arziki da siyasa na duniya.

Suma dai shugabannin Afirka ba a barsu a baya ba wajen gabatar da bukatun su ga taron na majalisar dinkin Duniya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gana da shugaban Amurka Joe Biden duk dai a kokarin ganin cewa Najeriya da Afirka sun samu mafita ta fuskar matsalolin dake damun su.

Masu harkokin kasa da kasa na ganin akwai bukatar samun mafita a wajen taron kamar yarda Dr. Elharon Mohammed ya shaida mana cewar ba lallai bane a samu sauyi a wannan taron, wannan zai zama kamar taro ne wanda aka saba yi kowa ya yi jawabisa, a kuma tashi duk da cewar dai agendar taron shine na inganta rayuwar karni, abunda kuma yake da mahinmanci kwarai.

A ranar 19 ga watan nan wato gobe Talatabne shugaba Tinubi zai yi jawabi a zauran taron da kuma ganawa da shugaba Biden na Amurka.

Wajen duba wasu kalubale da shugaba Tinubu ka iya fuskanta, Dr. Elharun ya ce babban kalubalen shine na juyin mulki a nahiyar Afirka wanda ke tadawa kasashen Turai hankali mai kassara demokiradiyya, wanda shine dalilin ganawarsa da shugaba Biden na Amurka. Tsoron da akeji shine kada taron ya zama na bada umarni mai makon na shugaba da shugaba.

To ko menene fatan sauran ‘yan Najeriya, Malam Abubakar Sada Babangida na fatan samun mafita ga talakan Najeriya da Afirka na samun tsaro, abinci, aikin yi da kuma makoma na gari.

Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibril:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like