Rabin ƴan matan Dapchi an tsallaka dasu zuwa jamhuriyar Nijar


Kusan rabin ƴan matan makarantar sakandaren Dapchi da aka sace daga makarantarsu  an tsallaka da su kan iyaka zuwa jamhuriyar Nijar.

Ƴan matan da ake zargin ƴaƴan kungiyar Boko Haram ake zargin sun sace su ne daga makarantar sakandaren Dapchi dake jihar Yobe.

 Wata majiya mai tushe ta shaidawa jaridar Daily Trust ajiya cewa an raba ƴan matan ya zuwa rukuni biyu, rukuni daya an ajiyesu a wani yanki dake arewacin jihar Borno ya yin da ragowar aka kai su wani ƙauye dake jamhuriyar Nijar.

An gano cewa ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Musab  Albarnawi dake biyayya ga ƙungiyar ISIS a yankin Afirka ta Yamma sune suka sace ƴan matan.

” An ɗauki ƴan matan cikin kwale-kwale ta wani ƙaramin kogi ana kuma riƙe da su a garin Duro dake kan iyakar jamhuriyar Nijar,”a cewar majiyar da ba ya so a bayyana sunansa.

Ya ƙara da cewa “Rukuni na biyu kuma an dauke su zuwa yankin Tumbin Gini a ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.”

You may also like