Shugaban sabuwar jam’iyyar APC wadda ta balle daga uwar jam’iyyar ta kasa, Mista Otunba Ajakaiye ya bayyana cewa sun yanke shawarar ballewa ne bayan an yi watsi da bukatarsu na neman Uwar jam’iyyar ta gudanar da Babban taronta na kasa don zaben sabbin shugabanni.
Ya ce, har yanzu jam’iyyar ba ta kaddamar da kwamitin amintattu na jam’iyyar ba. Daga cikin jigogin da suka halarci wurin kaddamar da sabuwar jam’iyyar har da Alhaji Dambabta Maikudi, Olorogun Omotejokwo Anababa sai kuma Ogbuefi Nwashiegokama.