Rahama Sadau Na Jin Haushi Ne Saboda An Koreta Daga Kannywood – Nafisa Abdullahi 


Surutun Da Rahama Sadau Ta Keyi Na Cewar ‘Yan Matan Hausa Film Nada Girman Kai, Tana Jin Haushi Ne Kawai Saboda An Koreta. 


Sananniyar ‘Yar wasan Hausa Film Nafisat Abdullahi ta mayar da martani akan kalaman da korarriyar jarumar nan Rahama Sadau tayi akan ‘yan Matan Hausa Film, inda ta zarge su da hassada da girman Kai.

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewar, kalaman da Rahama Sadau ta keyi  sambatu ne kawai na jin haushin korar da akayi mata a Masana’antar film, amma duk da haka ya kamata Rahamar ta sani cewar Matan Hausa Film sun wuce da tunanin ta, saboda Mata ne wayayyu masu ilimi wadanda suka fahimci rayuwa.

Indai jama’a basu mance ba, a wata tattaunawa da akayi da Rahama Sadau ta soki lamirin ‘Yan Matan Hausa Film, inda ta bayyana su a matsayin masu hassada da kyashi gami da girman kai, sannan tayi kira ga shugabannin Kungiyar ta Kanneywood dasu mike wajen magance matsalar. 

You may also like