Rahama Sadau Ta Nemi Gafarar Gwamnatin Kano Da Masarautar Kano Kan Wakar Da Tayi Da ClassiqFitacciyar jarumar finafinan Hausa da aka kora, Rahma Sadau ta nemi gafarar gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusu II kan wakar saba shari’a da al’adar Hausa da ta yi da mawaki Classiq, wanda hakan ya jawo aka kore ta daga masana’antar fim.

Jarumar ta nemi gafarar ne a wani shiri na ‘Ku Karkade Kunnuwanku’ wanda ake gudanarwa a wani gidan rediyo mai zaman kansa dake Kano, inda ta nemi masoyanta da sauran al’umma da su yafe mata kuma ba za ta sake aikata hakan ba.

You may also like