Rahoto: Albashin Sojoji Da Ƴan Majalisa A Najeriya


Sanatocin mu na zaune a majalisa suna wasa suna dariya ana ba su albashin Naira Miliyan 13 kowane wata. Abinci mai kyau, wajen kwana mai kyau, tufafi mai kyau, ga kyakkyawan tanadi ga iyalan su.

Amma Sojojinmu sun sayar da rayuwarsu saboda Najeriya. A harbe su, a yanka su, a kuma raunata. Mafi karancin albashinsu Naira 54,000, ba cikakkiyar kulawa da iyalan su. Ba kyakkyawan tanadi ga makomar rayuwar su.

Kuma duk da haka da wuya ka ji Sanata daya ya mike a majalisa domin kawo wani kudiri da zai amfani rayuwar sojojin mu.

You may also like