‘Yan uwa musulmi almajiiran Shaikh Ibrahim Zazzaky sun gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haifuwar Annabi Isa Almasihu (AS) a Yola.
Babban malami mai jawabi a taron, Muhammad Tukur Abdulhamid ya ce da Musulmi da Kirista kowa zai yi riko da karantarwar da ke cikin litatafinsa; ba za a samu sabani a tsakanin bangarorin biyu ba.
Ya ce matsalolin da ake samu ana samun su ne sakamakon kauce wa karantarwar Manzannin biyu.
Ya ce shigo da son zuciya da watsi da karantarwar ke haifar da rigingimu a tsakanin jama’a, don haka koma wa karantarwar Manzannin shi zai kawo karshen matsala tsakanin Musulmi da Kirista a kasar.
“Da muna aiki da karantarwar litatafan nan biyu, wallahi da ba wani Musulmi da zai nuna ma Kirista yatsa, haka da babu wani Kirista da zai nuna ma wani Musulmi yatsa, da ba mu samu kanmu cikin yanayin da mu ke ciki ba.”
Da ya ke gabatar da nashi jawabin, shugaban kungiyar kiristoci ta jihar (CAN), wanda Pasto Sunday Festus ya wakilta, ya ce taron yana da muhimmanci don haka bai kamata a shirya sau guda a shekara ba, ya ce sau uku ya kamata a shirya a shekara.
“Zaman lafiya shi muke bukata, muna fatan za ku a ci gaba da shirya wannan taron domin komai ibadar da kake yi ko kana kwana a Masallaci ko ka na kwana a Coci, idan ba ka neman dan uwanka da zaman lafiya to, ka yi a banza; ba bautar Allah ka ke yi ba”.
Shi kuwa Malam Bappari Umar Kem, daga Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ya yaba da shirya taron da matasan su ka yi inda ya ce bisa la’kari da halin da kasar take ciki taron ya zo a lokacin da ya dace.
Tun da farko a jawabinsa, shugaban taron kuma shugaban cibiyar sasanta tsakanin musulmi da kirista (Interfaith Group) Alhaji Abdullahi Njidda Damare, ya ce wajibi ne a ci gaba da shirya irin wadannan taruka domin kuwa ita ce hanyar samun fahimtar juna.
“Idan muna kusantar juna haka, za mu samu damar da za mu hadu mu warware ko wace irin matsala in ta taso tsakaninmu, zamu warware kowane irin rikici ne kuwa”.