Rahoto: Babu Motar Kashe Gobara Daya Mai Aiki A Zamfara 



Wani abu da ke zama babban sakaci da rashin kula da hakkokin al’umma daga gwamnatin jihar Zamfara shi ne irin yadda gwamnatin ta kasa yin wani tanadi a kan kashe gobara a gidaje, shaguna, da ma’aikatu ko da za a samu aukuwar gobara. Ba a fata! 
Babban abin da ke nuni karara daga sakacin gwamnati shine irin yadda babban dakin ajiye magani, da motocin hukumar ZAMSACA na jihar Zamfara suka ci suka cinya, aka tabka mummunan asara, babu wani dauki ko agajin gaggawa daga hukumar kashe gobara ta jihar, sakamakon babu kayan aiki masu rai a hukumar. 
Wani abin ban haushi tsakanin ofishin kashe gobara na jihar da ofishin ZAMSACA bai wuce Mita 40-50 ba, amma ana ji ana gani aka bar wuta ta kona dimbin dukiya saboda babu motocin kashe gobara ko daya mai aiki a Zamfara kuma ga shi wutar ta fi karfin al’umma . 
Akwai bukatar gwamnatin jihar Zamfara ta yi karatun ta natsu, domin ta sani wajibi ne ga kowacce gwamnati ta dauki matakai na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma motocin kashe gobara na da muhimmanci sosai wajen kai dauki a yayin gobara, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. 
A bangaren al’umma su kuma wajibi ne mu kauce wa duk wani abu dake saurin kawo gobara, domin kula da rayuwar mu da dokiyoyin mu. Ba wai komai sai mun jira gwamnati ta yi mana ba . 
Ya kamata mu hada karfi mu ya mu da masu arziki cikin mu a hada a sayi abubuwan da ake iya saye domin kai ma juna dauki kafin taimakon gwamnati ya iso. 
Muna wadannnan kiraye kiyaye ne, domin cigaban al’umma ba wai siyasa ba. Allah ya ganar da mu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like