Rahoto : Bayyanar Kungiyar Masu Da’awar Babu AllahA yunkurin Shedan na kautar da Mutane daga tafarkin Allah zuwa ga wutar Jahannama, a halin yanzu akwai wata kungiya da take watsuwa kamar wutar daji a cikin al’ummar mu. wadansu mutane ne da a turance ake kira “Atheists” (ma’ana, basu yarda da kasantuwar Ubangiji ba). 
Kungiya ce mai matukar hadari wadda a yanzu suna da reshe a nan Kano da Nijeriya baki daya. Suna nan a jami’o’in mu, fal; Farfesoshi, Daktoci dama dalibai, sun kuma soma shiga makarantun sakandare. Abin takaicin shine yadda suke jan mabiya wadanda suka kasance ‘yan uwanmu ne Musulmai.
Ko a jihar Kano an samu wani Mubarak Bala wanda dan manyan mutane ne masu mutunci da ya addini hidima, ya yi da’awar babu Allah, ya na ta kuma yada wannan akida a kafafen sadarwa na zamani da tare da shakka ba.

You may also like