Rahoto: Sammu Akayi Wa Buhari Ko Jifan Sa Akayi? 


Daga Nasiru Salisu Zango. 

Ya tsaya takara sau uku muna cewa magudi aka yi masa. Muka yi ta zage zage saboda mun dogara da shi cewar shi kadai ne mai gaskiya. Muka ringa yi masa kamfen ba dan samun kudi ba sai domin tunanin shi kadai ne zai cece mu. Fusatar ta yi yawa domin har barazanar tashin hankali wasu suka yi. Kyauta muka ringa fadar halayensa nagari da yawa daga cikin halayen nasa ma bamu san su ba gaya mana ake yi, amma saboda mun yi imanin cewar shine kadai mai gaskiya wanda zai iya yi mana maganin berayen da suka hana kasar mu sakat, wannan yasa muka dogara gareshi. 
Har lakabi muke masa iri iri lakabin da ya fi burge ni shine FIYA-FIYA maganin manya da kananan kwari. Da aka yi zabe aka ce bai ci ba,anan muka nuna hakurin mu ya kare, wasu daga matasa suka kwashi makamai suka ringa kashe junansu, tare da kone-konen dukiyoyin al’umma. Muka ringa saka kudin mu muna sayen wani kati domin taimaka masa wajen kamfen tunda mu a zaton mu ba shi da kudi, balle iyalinsa, shima ya fito ya gaya mana cewar da kudin bashi ya sayi takardar yin takara.
 Amma mu wacce sakayya aka yi mana?

1. Sakayyar farko karin farashin mai wanda ya haddasa tashin kayan masarufi.

2. Janye tallafin Dala yanzu ta koma 490 lokacin da muka zabe shi nawa dalar take? 

3. Shinkafa nawa ce yanzu? Meke faruwa ne? 

4. Ga wasu da ake zaton sunyi sibaran nabayye ance a tuhume su shi kuma ya basu kariya.

Anya kuwa ba asiri aka yi wa Baban nan namu ba? Ko da yake dama dogaro ga Allah shine mafita amma idan ka dogara ga mutum babu tabbas.

You may also like