Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya musanta rahotannin cewa ya samu baraka da gwamnonin PDP da kuma Shugaban jam’iyyar na Kasa, Uche Secondus.
A cikin wani jawabi da ya rabawa kafafen Yada Labarai, Tsohon Shugaban ya bayyana wadannan rahotannin a matsayin marasa tushe inda ya nuna cewa an kirkiri labarin ne don a janyo rudani tsakaninsa da gwamnoni. Ya kuma tabbatar da cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da shugabannin PDP.