Bincike ya nuna cewa yin amfani da magogin hakuri mai kaushi na zamani bai goge hakora da kyau sannan kuma yana da illoli da dama wajen raunana hakora. Da farko dai Amfani da magogin zamani mai karfi na matukar lalata dasashin hakora wanda kuma hakan na haifar da illoli kamar haka:
- Idan dasashin hakora ya samu rauni, kwayoyin cuta na samu damar amfani da kafafen da suka bude wajen shiga cikin jinin mutum ta yadda za su iya kaiwa ga zuciya.
- Idan dasashin hakora ya samu rauni, a kodayaushe zai rika yin jini kuma hakoran za su yi rauni
- Idan dasashin hakora ya samu rauni, hakoran zai canja launi zuwa kore-kore