Raila Odinga ya janye daga shiga zaben shugaban kasar Kenya da za a sake yi


Jagoran yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga, ya janye daga zaben shugaban kasar da za a sake yi wanda aka shirya gudanarwa ranar 26 ga watan Oktoba.

Kotun kolin kasar ta Kenya ce ta soke zaben kasar da aka gudanar cikin watan Agusta, inda tace zaben na cike da kurakurai.

Wannan ne dai karo na farko a nahiyar Afirka da wata kotu ta soke zaben shugaban kasa.

Da yake bayyana dalilinsa na janye wa daga zaben da za a sake yi Odinga yace har yanzu hukumar zaben kasar bata gudanar da sauye-sauyen da za su kaucewa faruwar matsalolin da suka da bai baye zaben farko da aka gudanar ba.

Odinga ya shawarci yan kasar ta Kenya da su bazama kan tituna domin bukatar kawo canji a tsarin zaben kasar.

Kafin a soke zaben shugaba mai ci,Uhuru Kenyatta, shine aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like