Rambo, Mashahurin Mai Satar Mutane Ya Shiga Komar Jami’an Tsaro


Jami’an rundunar hadin gwiwa mai aikin yaki da satar mutane da garkuwa da su (IRT), sun samu nasarar kama wani hatsabibin dan fashi da ya yi kaurin suna wajen satar mutane, mai suna Barau Ibrahim, wanda ake yi wa lakabi da Rambo.

Rahotanni na bayyana cewa, Rambo ba boyayye ba ne a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da jihar Zamfara, inda ya ke jagorantar wasu gungun ‘yan bindiga suna satar mutane da neman kudin fansa.

An kama shi da wasu bindigogi kirar AK47 guda biyu da abin jera albarusai biyu da kuma harsasai masu rai 51.

Kakakin rundunar Operation Absolute Sanity wanda babban sufeton ‘yan sanda ya kafa ya bayyana cewa an kama Rambo ne a yankin Mararrabar Yakawada dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

An kama Rambo ne tare da wani abokin harkar sa Shehu Abdullahi wanda ake yi wa lakabi da Gashin Baki mai shekaru 40, da wasu bindigogi da mota kirar Volkswagen Golf wacce aka ce mallakin Rambo ce.

Rundunar ta ce, an kama wadannan gaggan ‘yan bindiga sakamakon kokarin da jami’an rundunar ta IRT ke yi ba dare ba rana don maganin masu satar mutane da neman kudin fansa.

You may also like