RANA MAI KAMAR TA YAUWannan Rana ce da  mutan jahar Yobe ba zasu manta da ita ba. A wannan Ranar Boko Haram sukayi yunkurin kwato gidan gwamnatin jahar. 

A wannan rana hankulan Al’umma ya tashi sosai, miliyoyin ‘yan jahar Yobe sun Shiga fargaba sakamakon yadda mayakan Boko haram suka karbi ikon garin na Damaturu. 

Mutane da dama sun arce domin tsira da rayuwar su, jiragen yaki sunyita shawagi suna dauki ba dadi da mayakan kafun daga bisani a sanya dokar hana fita. 

Wannan rana ta lankome rayukan mutanen da basuji ba, ba su gani ba. 

Muna rokon Allah ya sake kwararo zaman lafiya mai daurewa a kasar mu baki daya.

You may also like