Ranar Hijabi ta Duniya 2023An ƙirƙiro ranar ce a wani yunƙuri na bunƙasa ƴancin gudanar da addini da fahimtar juna, inda akan ƙarfafa wa mata gwiwa wurin yin amfani da hijabi.

Ranar na zagayowa ne a ɗaya ga watan Fabrairun kowace shekara.

Taken ranar na wannan shekara shi ne ‘ci gaba, a madadin danniya’.

Wata ƴar Pakistan mai zama a Amurka, Nazma Khan ce ta ƙirƙiri ranar a shekarar 2013, bayan da ta fahimci cewa ba ita kaɗai ce take fuskantar ƙalubale ba saboda tana amfani da hijabi domin rufe sumarta.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like