A wani bangare na bukukuwan cika shekaru 56 da samun ‘yancin kan Najeriya, rundunar sojin kasar ta saki mutane 348 da ake tsare da su a jihar Borno bisa zarginsu da alaka da kungiyar ta’adda ta Boko Haram.
An saki mutanen a dandalin Ramat Square bayan an tabbatar da tantance su cewa, ba su da alaka da kungiyar.
Mutanen sun hada da maza 114, mata 107 da kuma yara kanana 127.
Kwamandan runduna ta 7 ta rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Victor Ezugwu ya ce, sojin sun saki mutanen ne bayan umarnin da suka samu daga shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya Yusuf Tukur Buratai.
Mutanen an kama su ne a wurare daban-daban inda aka kuma saki duk wadanda ba su da laifi.
An dai milkawa gwamnatin jihar Borno mutanen baki daya.