Rasha na daf da karbe iko da birnin Bakhmut | Labarai | DWFadar Kremlin ta ce a yanzu haka dakarunta suna daf da kwace iko da birnin na Bakhmut mai matukar mahinmanci ga Ukraine inda sojojinta suka rufe duk wata hanya mai shiga birnin tare da katse yiwuwar kai dauki wa lau ta sama ko ta kasa ga sojojin Kiev.

Dama dai masu aiko da rahotanni sun ce a ‘yan kwanakin nan dakarun Rasha da na kungiyar Wagner sun matsa lamba a Bakhmut inda suka kame wasu mahinman gurare dake tsakkiyar birnin bayan sun yi wa dakarun Ukraine barna mai yawa.

A ranar Litinin da ta gabata ma shugaban yankin Donesk dake karkashin ikon Rasha Denis Pouchiline ya wallafa wani faifan bidiyonsa yana kewayawa a tsakiyyar birnin na Bakhmut inda ya ce nan dan lokaci birnin zai dawo karkashin ikon Rashar. 

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like