Rasha na son tura wa Mali da takin zamani | Labarai | DWWata sanarwa da fadar shugaban Rasha Putin ta fitar, taa nunar da cewa ya tattauna da shugaban mulkin sojin kasar Mali ta waya Assimi Goita, inda Putin ya ce a shirye yake ya raba kimanin tonne dubu 300 na takin ga kasashen da ke bukata ciki har da Mali.

Kanal Assimi Goita ya rungumi Rasha hannu bi-biyu bayan da ya raba gari da Faransa, inda baya ga fannin tsaro yake neman kyautata alakar Mali da Rasha a sauran fannonin.

 You may also like