Kasar Rasha ta ce Sojan Amurka sun kai wani samame kasar Syria inda suka kashe sojojin Syria 60, kamar yadda majiyoyin samun labarai suka karas.
Wata sanarwa da Sojan Rasha suka fitar na cewa akwai wasu tarin sojoji na Syria da suka jikkata a harin na yau.
A cewar Sojan Rasha lamurra a kasar Syria na kara dagulewa saboda yadda ‘yan tawaye ke zafafa kai hare-hare, sannan kuma muddin yarjejeniyar tsagaita wuta ya ci tura kasar Amurka ke da laifi.
Wani Babban Hafsan sojan Rasha Vladmir Savchenko ya bayyana haka a wata tattaunawa da akayi dashi a gidan TV na Moscow.
Ya bayyana cewa cikin saoi 24 da suka gabata an zafafa kai hare hare domin akalla wurare 55 mallakin Gwamnati da na fararen hula aka kaiwa hari.
Fararen hula akalla 12 suka gamu da ajalinsu yayin hare-haren.