Rasha ta soke yarjejeniyar Nukiliya da Amurka


 

 

 

Shugaban Rasha, Vladmir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ta dakatar da yarjejeniyar watsi da makami mai guba da kasar ta cimma da Amurka a shekarar 2000.

Dokar wadda shugaba Putin ya rattaba mata hannu a wannan litinin ta kuma zargi Amurka da haifar da barazana ga Rasha sakamakon wasu halaye na kiyayya da ta ke nuna mata, abin da Rashan ke kallo a matsayin baraza a gare ta.

A karkashin wannan yarjejeniya da kasashen biyu suka cimma kimamin shekaru 16 da suka gabata, kowacce daga cikinsu za ta yi watsi da tan 34 na sinadarin Plutonium ta hanyar babbaka shi a injin sarrafa makamin Nuikiya.

Wannan dai na cikin matakin rage karfin makaman Nukiliya.

A cikin shekarar 2010 ne, kasashen biyu suka jaddada yarjejeniyar, yayin da Amurka ke cewa, jumullar tan 68 da kasashen biyu za su kona, sun isa a samar da kayan kera makaman Nukiliya har dubu 17.

To sai dai fadar Kremlin ta bayyana cewa, za ta mutunta yarjejeniyar da zarar Washington ta janye takunkuman da Moscow ke kallo a matsayin kiyayya a gare ta.

Moscow dai ta ce, dole ne ta dauki matakan tsaro don kare kanta saboda yadda Washington ta gaza aiwatar da sharuddan yarjejeniyar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like