Rashawa: Gwamnatin Katsina Za ta Ladaftar Da Jami’an Jin Dadin Alhazai 


Gwamnatin Katsina za ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki koke koken da aka gabatar na yadda wasu jami’an Jin dadin Alhazai na jihar suka rika damfarar Alhazai a lokacin aikin hajjin bana.

Gwamnan Jihar, Alhaji Bello Masari ya nuna takaicinsa bisa irin wannan dabi’a ta jami’an wadanda aka dora alhakin kula da Alhazai don samun damar sauke farali na Ubangiji inda ya yi alwashin hukunta duk wani jami’i da aka samu da laifi sannan ya nuna cewa za ta kafa wani sabon kwamiti wanda zai kula da aikin hajji na shekarar 2017.

You may also like