
Asalin hoton, Getty Images
Marcus Rashford ya fara motsa jiki a Carrington, bayan raunin da ya ji a FA Cup a wasan da Manchester United ta doke Fulham.
Dan kwallon ya ji rauni a karawar da United ta ci 3-1 ta kai daf da karshe a FA Cup daga nan aka shiga kwanatin buga wasannin neman shiga Euro 2024.
Tun farko tawagar Ingila ta gayyaci dan wasan, wadda ta dauka yana da koshin lafiya, wadda ta je ta ci Italiya 2-1 da doke Ukraine a Wembley 2-0.
Ingila ta hada maki shida a wasa biyun da ta buga a rukuni, domin neman shiga gasar nahiyar Turai da Jamus za ta karbi bakunci a 2024.
Dan wasan na yin atisaye shi kadai, baya buga tamaula tare da ‘yan wasa har sai ya ji kwari a jikinsa.
Mai shekara 25 ya ci Real Betis kwallo na 27 a United a kakar nan, wanda ya ci kungiyar Sifaniya gida da waje a Europa League.
Rashin koshin lafiyar Rashford kan iya sa fargabar ko zai iya buga wasan da Manchester United za ta yi da Newcastle United ranar Lahadi a Premier.
Dan wasan ya zura kwallo na biyu a ragar Newcastle United da kungiyar Old Trafford ta lashe Carabao Cup na bana.
Wasan da kungiyoyin za su yi a St James zai kara fayyace wadanda za su ci gaba da zama a cikin yan hudu a teburin Premier League.
Manchester United tana mataki na uku mai maki 50, ita kuwa Newcastle United mai maki 47 tana ta biyar a teburin bana..