Rashin aikin yi a Najeriya ya karu da kaso 1.2


 

 

Mutane miliyan 106.69 masu shekaru 15-64 ne ba su da aikin yi a Najeriya a watanni 3 na biyu na shekarar 2016 wanda yakaru da kaso 0.65 idan aka kwatanta da na watanni ukun farko na shekarar.

A sanarwar da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar ta bayyana cewa, adadin wadanda ba su da aikin yi a Najeriya ya karu da kaso 1.2 a watanni uku na 2 n shekarar 2016 inda ya kama kaso 13.3 wanda wannan lokacinda hakan ya kai kololuwa tun shekarar 2009.

Haka zalika adain wadanda ba su da aikin yi ta karu da kaso 12.2 wato mutane miliyan 10.644 wanda hakan ke nuna rashin aikin yin ya karu da kaso 0.06 wanda ya kai mutane miliyan 69.04. Kuma yawan masu neman aiki a kasar ya kaimutane miliyan 79.9 wanda ya karu da kaso 1.78. Rashin aikin yi a tsakanin matasa kuma ya karu da kaso 24 cikin 100.

Hukumar ta bayyana adadin wadanda ba su da aikin ne duba da mutanen da suka je neman aiki a cikin awanni 20 na makon da ta yi nazarinta.

Daga shekarar 2015 zuwa yau kusan mutane miliyan 4 n3 suka rasa aiyukan yi wadanda kuma sukashiga kasuwar neman aiki a Najeriya.

You may also like