Rashin Bayyana Osinbajo A Matsayin Muƙaddashin Shugaban Ƙasa A Wasiƙar Tafiyar Buhari Ya Jawo Cece – kuce A MajalisaA jiya Talata ne shugaban majalisar dattija Sanata Bukola Saraki ya karantawa zauren majalisar wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika masu kan sake komawa birnin London domin a duba lafiyarsa.

Sai dai karanta wasiƙar ke da wuya muhawara ta barke tsakanin ƴan majalisar, bisa abinda wasunsu suka kira da rashin bayyana mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da Buharin bai yi ba a matsayin muƙaddashin shugaban ƙasa, a fayyace.

Cikin wasikar dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ambata cewa babu kayyadajjen lokacin da zai dawo gida, dan haka mataimakinsa farfesa Osinbajo zai cigaba da kula da al’amuran tafiyar da gwamnatin kasar, kamar yadda sashi na 145 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada dama.
Al’amarin da ya janyo kace-nace tsakanin waɗanda ke ganin kamata ya yi a ce shugaban ya fito fili wajen ambata Farfesa Osinbajo a matsayin muƙaddashin shugaban kasa.

You may also like