Rashin jituwar ma’aurata:Ina mafita 


Hoto:Daily Trust

Abu ne sananne cewa a wannan zamani, duniyar Bahaushe – har da ta wanda ba Bahaushe ba – ta cika da rikita-rikita da rikice-rikice tsakanin ma’aurata. Aure kuwa abu ne mai muhimmanci wanda ya kamata a gina shi kan soyayya da kauna. To amma wace irin soyayya? Ba soyayya ta shakaka ba; soyayya ta hakika. A yanzu, lamarin yana da takaici matuka!

Za ka ga kafin a yi aure, ana ta soyayya tiryan-tiryan kamar ba gobe. Amma da zarar an yi aure, sai husuma ta fara tashi kamar wutar daji. To ita wannan matsala idan mutum zai dauki matakai na kiyaye ta, to zai iya kawar da su daga gare shi cikin ikon Allah. Wannan makala za ta amfani kowa – Musulmi ko Kirista.

Da farko, auren mace don kyawun fuskarta yana da matukar illa, domin bayan an yi aure, kyawun zai iya gushewa. Shi ke nan kuma! Da ma don kyawun aka yi auren, yanzu kuma babu kyawun. To a nan sai soyayya ta dawo tsana. Koman kyawun ‘ya mace, mafi akasari tasirinsa kafin ta yi aure ne – tana yin aure, kyawun halinta ne zai yi tasiri. Saboda haka kar kyau ya zama ma’auninka na auren mace. Na yi amanna cewa wannan shawara ba Musulmi kadai za ta amfana ba, har da Kiristoci.

Bugu da kari, shi rikici ba a rasa shi kwata-kwata a tsakanin ma’aurata. To idan aka samu wannan dan rikici, ba shi ke nuna cewa aure ya zo karshe ba. Akwai hanyoyin shawo kan matsalar. Muhsin Ibrahim, malamin harshen Hausa a Jami’ar Cologne da ke Jamus, ya bankado yadda lamarin yake, inda ya ce: “Sirrin zama da iyali cikin farin ciki ba abu ne boyayye ba. Rikici kuwa abu ne da ba a rabuwa da shi, wanda ke sauya rayuwar kunci ta koma ta farin ciki.” Ya kara da cewa: “Kar dai a bar rikicin ya yi kamari. Ku hadu domin tattauna matsalolinku.” Ka ga ke nan a kullum tattaunawa na da muhimmanci domin ta hanyar haka ne kowa zai gano matsalolin kowa.

Kuma wasu lokutan, tun kafin a yi auren, auren yake wargajewa. Ba komai ke janyo haka ba sai aikata abubuwan da ba su halatta ba a tsakninku kafin aure. Shi ya sa za ka ga bayan an yi aure, kowa na zargin kowa; kowa yana yi wa kowa kallon hadarin kaji. Ita matar babu hali mijinta ya fita waje sai ta zarge shi da aikata irin abin da suka saba aikatawa kafin su yi aure. Haka shi ma mijin. Daga karshe, sai ka nemi auren ka rasa.

Idan ba a dauki mataki ba, adadin zaurawa tsakanin al’ummar Hausawa sai ya fara gogayya da adadin ‘yan mata, wadanda ba su taba yin aure ba, domin saki ya zama ruwan dare a yanzu. Kuma wani abin bakin ciki shi ne: za ka samu abin da ke kawo sanadin sakin bai taka kara ya karya ba. ‘Yar matsala kadan saki, saki, saki! To idan ka sake ta fa, a banza za ka dinga kashe kudin da kake samu na albashinka.

A karshe, babban maganin duk wata matsala shi ne “HAKURI”.

Muhammadu Sabiu ne ya rubuto wannan makala daga Bauchi. 09078713542


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like