Rashin kyawun yanayi ya tilastawa Buhari tafiya Daura daga Kano a Mota


Shugaban kasa Muhammad Buhari ya tafi Daura mahaifarsa dake jihar Katsina  daga Kano a mota saboda rashin kyawun yanayi.

Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasar ya bayyana haka cikin wata wata sanarwa da yafitar ranar juma’a.

Ya ce Buhari ya tafi Daura ne daga Kano inda ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

” Halin da yanayi ke ciki ya jawo tafiya zuwa Daura a mota,” yace.

Shehu ya kuma ce Buhari ya samu rakiyar gwamna  Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da kuma gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar.

A Katsina ya samu tarba daga gwamna Aminu Bello Masari  da kuma mai martaba sarkin Daura Alhaji Umar Faruk.

Kafin barinsa Kano sai da shugaban ya bude wasu masana’antu guda.

You may also like