Rashin Lafiya Da Tsaro Ne Zasu Hana Ni Zuwa Kano – Kwankwaso


Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa rashin lafiya da kuma sha’anin tsaro ne za su hana shi ziyarar Kano a karshen wannan watan don kaddamar da Gidauniyar Kwankwasiyya kamar yadda aka tsara.

Wata majiya daga Kaduna inda Kwankwaso ya gudanar da taro da jigogin Kwankwasiyya ta nuna cewa tsohon Gwamnan ya tabbatarwa wadanda ke wurin taron cewa ya samu rahoton tsaro na yiwuwar barkewar tashin hankali a yayin ziyarar sannan kuma shi kansa ba ya Jin dadin jikinsa wanda kuma ya nemi a soke ziyarar zuwa wani lokaci daban.

Haka ma, Kwankwaso ya nuna rashin Jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da harkokin tafiyar Kwankwasiyya da kuma irin kalaman da ke fitowa daga bakin magoya bayansa.

*
Kun gamsu da wadannan uzurori na Kwankwaso na soke wannan ziyara zuwa Kano?

You may also like