Rashin Lafiyar Buhari  Ta Hana A Gudanar Da Babban Taron Jam’iyar APC Na Kasa – Yari 


Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya alakanta rashin lafiyar shugaban kasa Muhammad Buhari da jinkirin aka samu nayin babban taron jam’iyar APC na kasa. 

 Yace rashin bayyanar shugaban kasa Muhammad Buhari yasa bazai yiwuba a gudanar da babban taron ba. 

Yari ya bayyana haka ranar Laraba a wani taron manema labarai na hadin gwiwa shida mai magana da yawun jam’iyar APC, Bolaji Abdullah, a Sakatariyar uwar jam’iyar dake Abuja. 

” Mun dade muna tattauna maganar babban taron amma kuma kunsan shugaban kasa shine uban jam’iyar na kasa, na farko kafin babban taron akwai tsare-tsare  da yakamata ayi, kwamitin gudanarwar jam’iyar na kasa dole sun cimma matsayar rana, a lokaci guda kuma dole mu amince da rahoton na kwamitin gudanarwar jam’iyar kuma a matsayin shugaban kasa na uban jam’iyar dole yana cikin kwamitin, Kun dai san halin da shugaban kasar ke ciki a yanzu. 

“Mun dade muna saka rana amma saboda rashin lafiyarsa mun kasa gudanar da taron amma dole kawo wani tsari da zai bamu damar gudanar da taron, amma bana zaben shugabanni ba.”

Yari yace shugabannin jam’iyar zasu gana da mukaddashin Shugaban kasa kan maganar 

You may also like