Rashin Samun Cikakken Goyon Baya Ya Sa Muƙarraban IBB Suka Ƙaryata Wasiƙarsa Ga Buhari – Afegbua


Kakakin Tsohon Shugaban Kasa, Kassim Afegbua ya jaddada cewa Ibrahim Babangida ne ya bashi umarnin bayyana matsayinsa kan salon mulkin Shugaba Buhari inda ya nemi Shugaban ya jingine batun sake tsayawa takara.

Ya ce, ya kwashe shekaru 13 yana yiwa tsohon Shugaban kasar aiki kuma bai taba fitar da wani bayani daga Shugaban ba sannan daga baya ya musanta ba sai a wannan karo da abokansa suka karyata wannan wasikar kan cewa ba da yawun bakinsa ba ne aka fitar da ita saboda sun ga jama’ar kasa sun yi Allah wadai da wasikar.

You may also like