Rashin Taki Ne Babbar Matsalar Manoman Nijeriya


 

Wani fitaccen manomi, Malam Abubakar Dandada ya bayyana cewa rashin takin zamani da karancin maganin feshi da sauran kayayyakin amfanin gona na daya daga cikin manyan matsalolin da suka addabi mafi yawan manoman Nijeriya.

Malam Abubakar ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP HAUSA a ofishinsa da ke Bauchi a kwanakin baya.

“Nijeriya tana daya daga cikin manyan kasashe da Allah ya albarkace ta da fadin kasa duk abin da mutum ya shuka sai ya fito kuma da yawa daga cikin mutane sun yi watsi da noma a shekarun baya. Amma sakamakon tsadar kayan abinci da aka fuskanta a wannan shekara idan ka samu mutum 10 takwas daga cikinsu sun yi noma a wannan shekara”.

Malam Abubakar, wanda har ila yau shi ne shugaban jam’iyyar adawa ta NDP, reshen Jihar Bauchi, ya kuma nuna muhimmancin gwamnatocin jihohin kasar nan da na kananan hukumomi su rika baiwa manoma taki a kan lokaci domin ta haka za a bunkasa harkokin noma da kiwo a Nijeriya.

“Na gamsu da manufofin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari game da matakin da ya dauka na bunkasa aikin noma domin babu wata kasa da za ta samu ci gaba da bunkasar tattalin arziki matukar ba ta iya ciyar da kanta.

“Na shuka shinkafa, masara, gyada, waken suya, dawa, wake da sauran kayan abinci kuma na kashe sama da naira miliyan biyu a wannan shekara kullum sai ka samu masu aiki a gonana da ke kan hanyar Maiduguri, wani lokaci za ka samu sama da mutum 40 suna aiki a gonana”.

Daga karshe ya yi amfani da wannan dama inda ya bayyana cewa “hanya daya tilo na farfado da tattalin arzikin kasar nan shi ne a rike noma da kiwo tsakani da Allah kuma dole matasa su cire lalaci a zuciyarsu”.

You may also like