Rashin Tsayayyun Iyaye Ya Tagayyara Rayuwar Wata Matashiya


Wata matashiyar budurwa da ke son ta yi rayuwa tagari ta kai kanta ga hukumar Hisbah da ke jihar Kano, inda ta nemi a taimaka a gano mata iyayenta, domin samun kulawa da tarbiyyar da ta dace.

A jawabin da wannan yarinya da aka sakaye sunanta ta yi wa shugabannin Hisba na jihar Kano, ta koka da irin halin kunci da ta samu kanta da yadda wasu batagari suka yi kokarin lalata mata rayuwa.

Ta ce, ta nemi mahaifiyarta ta nemo mata mahaifinta, bayan da ta kai ta gidan kanin ta wanda shi kuma ya nuna muradinsa na son lalata da ita.

“Sai ya kira ni ya ce na zo na rika danna masa kafa, daga nan sai ya rika jawo ni jikinsa”.

Daga nan ta koma kauye wajen dangin mahaifinta wanda nan ma wata tsohuwa ta rika umartar ta da rika kawo mata kudi ba tare da ta dora mata kayan sayarwa ba.

Bayan ta gudu zuwa cikin birnin Kano wani ya hada ta da wata balarabiya wacce ya ce za ta rike ta kamar ‘yar cikin ta.

Ta ce,, “cikin dare sai ta zo tana shasshafa min jiki, wanda hakan ya sa na tsorata da safe na gudu. Daga nan sai dai na yi can na yi nan, da abin ya ishe ni shine na kawo kaina ga Hisbah don a nemo mahaifiyata ta nemo min mahaifina.”

Yayin da aka tambayeta ko ina mahaifiyar ta ta take, sai yarinyar ta kada baki ta bada amsar da taba kowa mamaki.

“Tana can Sabon Gari tana iskanci tana shan Giya”.

“Mahaifin naki fa yana ina?”

“Ban san Mahaifina ba”.

A karshe dai hukumar Hisbah ta yi alkawarin gayyato mahaifiyar ta da kuma binciko inda asalin mahaifinta yake.

You may also like