Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya tabbatar da cewa shi ya tsara hanyoyin da aka bi har mayakan Boko Haram suka amince da fara sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok.
Ya ce, shi da kansa ya gayyato kasar Swiss kan ta zama mai shiga tsakani sai kungiyar Red Cross wadda ita ce ta kwaso ‘yan Matam a cewarsa, shi ya hada ainihin mutumin da ya yi sulhun, Mustafa Zanna da jami’an gwamnatin Swiss da Red Cross.
Ya kara da cewa nan bada jimawa ba za a sako wasu ‘yan Matam saboda an samun amincewa a tsakanin gwamnati da Boko Haram inda ya kuma musanta Rahotanni cewa an yi musayar Matan ne da kwamandojin Boko Haram