Rayuwa A Arewa Ga Ya Mace Na Cike Da Kalubale- Rahma Sadau


“Rayuwa ga ya mace a arewacin Najeriya na da ke son ta zama wani abu a gaba na cike da kalubale” Rahama Sadau tace.

Jarumar ta bayyana haka ne cikin  wata tattaunawa da tayi da jaridar Thisday.

Sadau wacce kungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN ta kora daga  Kannywood biyo bayan fitowarta a cikin wata waka da shahararren mawakin nan da ake kira Classiq, yayi inda mutane da dama suke ganin jarumar ta wuce gona da iri.

Jarumar dai ta alakanta  shaharar da tayi da kuma nasarar da take samu da korarta da akayi daga Kannywood.

Tace korarta daga masana’antar da akayi ya bude mata damarmaki a masana’antun shirya finafinai dake cikin gida Najeriya da ma kasashen waje.

Amma kuma jarumar ta bayyana cewa a koda yaushe zata duba addininta da kuma inda ta fito kafin ta karbi wani matsayi a masana’antar shirya finafinai ta Nollywood ko kuma ko wacce irin masana’antar fim dake wajen kasarnan.

Sadau tun farko taki karɓar kwantaragin yin wani fim inda zata fito a matsayin me neman mata duba da addininta da kuma al’ada.

You may also like